Wasu Kungiyoyin Jami’o’i Sunyi Martani Kan Biyan ASUU

 

Gwamnatin Tarayya ta yi alkawarin ba Jami’o’i N40bn a matsayin EA.

Kungiyoyin SSANU, NASU, da NAAT sun ce su ba ayi masu adalci ba.

Sauran Ma’aikata sun ce ba za a yarda ASUU kadai ta tashi da 75% ba.

A ranar Laraba ma’aikatan jami’an gwamnatin Najeriya wadanda ba su koyarwa su ka gargadi gwamnati game da kudin da ta ke shirin biyan ASUU.

Kungiyoyin SSANU, NASU da NAAT na malaman fasaha da sauran ma’aikata jami’o’i su na kukan akwai rashin adalci wajen yadda za a raba wannan kudi.

Kafin ASUU ta janye yajin-aiki yau, sai da gwamnati ta yi alkawarin biyan jami’o’i Naira biliyan 40 a matsayin alawus din karin aikin da ake jibga masu.

A daidai lokacin da kungiyar ASUU ta bada sanarwar janye yajin-aiki, sai wadannan kungiyoyi su ka fito su na cewa an zalunce su sosai a kason da aka yi.

Jaridar Daily Trust ta rahoto kungiyoyin uku su na kukan cewa kungiyar ASUU ta tashi da 75% na wannan kudi, yayin da aka bar dukkansu da 25% kacal.

Shugaban NAAT na kasa, Kwamred Ibeji Nwokoma, ya ce duk wanda ke tunanin cewa sauran ma’aikata za su koma aiki a wannan tsari ya na mafarki ne.

A cewar Nwokoma, su na neman ganin yadda za su zauna da gwamnati domin shawo kan lamarin. Shi ma shugaban SSANU, Kwamred Mohammed Haruna Ibrahim, ya ce da wannan kaso, da alamu gwamnati ba ta neman ganin an zauna lafiya a jami’o’i.

Haruna Ibrahim ya ce dole sai dai a raba alawus din daidai wa-dai-da watau 50%-50%, domin ‘yan kungiyar ASUU ba su fi sauran ma’aikatan jami’an yawa ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here