Kungiyoyin Kwallon Kafa 10 Mafi Daraja a 2021

 

Kungiyar kwallon Manchester City ta zama kungiya mafi daraja a duniya.

An fahimci cewa darajar Man City ya hau ne bayan siyan sabon dan kwallon Ingila, Jack Grealish.

Kungiyar PSG sun shiga jerin kungiyoyin bayan siyan Lionel Messi daga Barcelona.

Kungiyoyin kwallon Firimiya Lig, Chelsea, Man City da Manchester United sun shiga jerin kungiyoyin kwallo mafi daraja a duniya.

Kungiyoyin Ingila biyu ke kan gaba a jerin.

A cewar Transfermarkt da ta tattara jerin, darajar jimillan yan kwallon Man City yanzu ya kai £955.6m.

SunSport ta ruwaito cewa sabon dan kwallon Ingila, Jack Grealish da Man City ta saya £100million ya bata wannan matsayi.

Chelsea ta zo na biyu sakamakon siyan dan kwallo Romelu Lukaku a farashin £97.5 million daga Inter Milan.

Hakazalika kungiyar kwallon PSG sun hau zuwa na uku bayan sayan gwarzon dan wasa, Lionel Messi.

Manchester United ta zo na hudu bayan sanar Raphael Varane daga Real Madrid da Jadon Sancho daga Borussia Dortmund.

Ga jerin kungiyoyin nan:

1. Man City (Ingila) – £955.6m.

2. Chelsea (Ingila) – £898m.

3. PSG (Faransa) – £894m .

4. Man United (Ingila) – £835m.

5. Liverpool (Ingila) – £814m.

6. Bayern Munich (Jamus) – £736m.

7. Real Madrid (Spain) – £700m.

8. Barcelona (Spain) – £694m.

9. Atletico Madrid (Spain) – £656m.

10. Tottenham Hotspur (Ingila) – £633m.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here