Abin Kunya Boko Haram Bata Zo Karshe ba – Gwamna

Kawo karshen Boko Haram yana daukar lokaci mai tsawo, cewar Gwamna Bala Mohammed.

Gwamnan jihar Bauchi, ya ce babban abin kunya ne ace har yanzu ba a fatattaki ‘yan Boko Haram ba.

Ya fadi hakan ne lokacin da kwamitin ‘yan majalisar wakilai suka kai masa ziyara Gwamna Bala Mohammed ya nuna takaicinsa a kan yadda yakar Boko Haram yake daukar lokaci mai tsawo.

Gwamnan jihar Bauchin yayin da kwamitin ‘yan majalisar wakilai a kan sojoji suka kai masa ziyara a gidan gwamnati a ranar Litinin, 9 ga watan Nuwamba, ya ce wannan babban abin kunya ne a ce har yanzu ba a kawo karshensu ba.

A cewar Bala; “Duk da mutum mai kwazo irin Femi Gbajabiamila ne ke jagorantar majalisar wakilan.

“Shiyasa mafi yawan ‘yan kwamitin ba daga arewa maso gabas suke ba.

“Ku taimaka, ku samar mana da kwanciyar hankali.

Idan ba a kawo karshen wannan al’amarin ba, zai zama abin kunya. An dade ana yin abu daya.”

Sannan ya yi tsokaci a kan tsanantuwar ‘yan ta’adda da masu satar shanu wanda ya janyo sojoji suna ayyukan ‘yan sanda, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

“Sojoji kullum bukatar makamai da kayan aiki suke yi, sun gaji, saboda ba za ka hada yawansu da na ‘yan Najeriya ba.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here