Bana Kunyar a Yada Hotona da Hushpuppi – Dino Melaye
Tsohon dan majalisar dattijan Najeriya, Dino Melaye, ya yi watsi da hasashen cewa yana jin kunyan hoton da ya dauka tare da dan damfara da aka kama, Hushpuppi.
Dan siyasar a cikin wata sanarwa ya bayyana cewa ba shi da dalilin boyewa saboda hoton da ya dauka tare da wani.
Read Also:
Ramon Olorunwa Abass, wanda aka fi sani da Hushpuppi, a yanzu haka yana fuskantar shari’a a wata kotun Amurka bisa zargin zamba Ga dukkan alamu, tsohon sanatan Najeriya, Dino Melaye, bai damu da yada hotonsa da ake yi ba tare da ɗan damfara, Ramon Olorunwa Abass, wanda aka fi sani da Hushpuppi.
Melaye a cikin wata sanarwa ta shafinsa na Facebook a ranar Asabar, 7 ga watan Agusta, ya musanta rahotannin da ke cewa ya yi kira ga jama’a da su daina yada hotunansa da fitaccen dan damfara.
Ya bukaci duk wanda ke son yada hotonsa da Hushpuppi da ya yi hakan.
Ya ce:
“Babu wani lokaci da na nemi mutane da su daina sanya hotunana tare da Hushpuppi ko wani don wannan lamarin saboda babu dalilin hakan.
“Ni mashahurin dan siyasa ne, don Allah a ci gaba da yadawa jare. Abun da tsuntsu ya ci da shi zai tashi. SDM ”