Cutar Kwalara ta yi Sanadiyyar Kashe Mutane 25 a Jahar Ogun
Cutar kwalara ta ɓarke a Ogun, inda aka tabbatar da ta kashe aƙalla mutum 25 a Magboro, karamar hukumar Obafemi-Owode a jahar.
Barkewar cutar ta shafi garuruwan Arepo, Akeran, Akintonde, Sofolarin da Abule – Oko na Magboro.
Kwamishinar lafiya, Dr Tomi Coker, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce, ya fi yawa a tsakanin masu kabu-kabu a yankin.
Mutane 25 ne ake fargabar sun mutu sakamakon barkewar cutar kwalara a Magboro, karamar hukumar Obafemi-Owode a jahar Ogun.
Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa barkewar cutar ta shafi garuruwan Arepo, Akeran, Akintonde, Sofolarin da Abule – Oko na Magboro, lamarin da ya haifar da fargaba a tsakanin mazauna garin.
Read Also:
Kwamishinar lafiya, Dr Tomi Coker, ta tabbatar da faruwar lamarin, inda ta ce, “ya fi yawa a tsakanin masu kabu-kabu a yankin.”
Shugaban Kwamitin Ci gaban Al’umma a Magboro, Oluwasegun Oladosu, ya shaida wa jaridar a ranar Talata cewa an samu asarar rayuka 15.
Ya kara da cewa kusan mutane 10, wadanda suka tashi daga garin zuwa Kara suma sun mutu sanadiyar cutar kwalara.
Oladosu ya ce masu sana’ar tuka babura sun fi kamuwa da cutar. Ya kuma ce an garzaya da yarinya ‘yar shekara takwas da ke fama da cutar kwalara zuwa asibitin al’umma domin yi mata magani.
Shugaban na CDC ya ce wata tawagar gwamnati ta ziyarci garin kuma ta ba da magunguna don maganin kwalara da rigakafin cutar.
Sai dai kuma ya yi kira ga gwamnati da ta tabbatar da cewa a koda yaushe tana aiwatar da shirin tsaftace muhalli a cikin al’ummar Hausawa, wanda ya yi wa lakabi da “mara tsafta.”