Cutar Kwalara ta Kashe Mutane 672 a Sudan

 

Kwalara ta kashe aƙalla mutum 672 daga cikin 24,00 da suka kamu da cutar a Sudan.

Wata jaridar birnin Paris, Sudan Tribune, ta ce an samu ɓarkewar kwalarar ne a jihohin Sennar da Gezira da kuma White Nile da ke tsakiyar ƙasar.

Maikatar lafiyar Sudan ta sanar da halin da ake ciki game da yaduwar cutar ne mako guda bayan ta karɓi tallafin rigakafin cutar kwalarar miliyan 1.4.

Jihohi 10 daga cikin 18 na ƙasar suna fama da yaɗuwar kwalara a ƙasar tun daga tsakiyar watan Agusta saboda mamakon ruwan sama da aka yi fama da shi.

Yaƙin basasar Sudan ya shafi ma’aikatar lafiyar ƙasar, inda hukumar lafiya ta duniya ta ce aƙalla kashi 80 na asibitocin ƙasar sun samu matsala.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here