Jami’an ‘Yan Kwana-Kwana Sunyi Nasarar Ceto Wata Dattijuwa a Rijiya

Jami’an hukumar Kwana kwana sun yi nasarar ceto wata dattijuwa mai shekaru 80 da ta fada cikin rijiya a Kano.

Dattijuwar wacce ke zaune a Tundun Wuzurchi ta fada cikin rijiyar ne a yayin da ta ke kokarin diban ruwa.

Bayan sanar da su, jami’an hukumar sun garzaya inda abin ya faru inda suka ciro dattijuwar da ranta suka danka ta hannun dan uwanta.

Hukumar kwana kwana na Jihar Kano, a ranar Juma’a, ta ceto wata dattijuwa mai shekaru 80 da ta fada a cikin rijiya a Tundun Wuzurchi a Municipal a Jihar Kano kamar yadda The Punch ta ruwaito.

Mai magana da yawun hukumar kwana kwana, Malam Saidu Mohammed cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, ya ce an kira hukumar daga Tundun Wuzurchi misalin karfe 6.40 daga wani Mallam Ibrahim Hussaini.

A cewar sanarwar, hukumar kwana kwanar ta aike da tawagar masu kashe gobara zuwa wurin, da isarsu wurin, sun gano cewa wata dattijuwa mai shekaru 80 ne ta fada cikin rijiya.

Sanarwar ta kara da cewa, “Jami’an na kwana kwana sun ceto dattijuwar da ranta, wacce ta fada cikin rijiya yayin da ta ke kokarin diban ruwa sannan suka mika ta hannun dan uwanta, Mallam Kabiru na Tudun Wuzurchi.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here