Rabi’u Kwankwaso ya yi Jimamin Mutuwar Farfesa Aminu Yusuf

 

Jami’ar Jihar Kaduna ta KASU, ta rasa Farfesa Aminu Yusuf Usman a karshen makon da ya gabata.

Rabiu Musa Kwankwaso Masanin tattalin arzikin yana cikin ‘yan kwamitin yakin neman zabensa.

‘Dan takaran shugabancin kasar ya aika sakon ta’aziyya ga iyali da ‘yanuwan Aminu Yusuf Usman.

Kaduna – A karshen makon nan ne jami’ar jihar Kaduna wanda aka fi sani da KASU, ta rasa kwararren malamin ta, Farfesa Aminu Yusuf Usman.

Rabiu Musa Kwankwaso mai neman takarar shugaban kasa a jam’iyyar NNPP, ya na cikin wadanda mutuwar Farfesa Aminu Yusuf Usman ta taba.

A wata sanarwa da ya fitar a yammacin Lahadi, 22 ga watan Junairu 2023, Rabiu Musa Kwankwaso ya yi jimamin mutuwar shehin malamin.

Da yake magana a dandalin Twitter, Sanata Kwankwaso ya shaidawa cewa malamin jami’ar yana cikin ‘yan kwamitin yakin neman takarar da yake yi.

Ta’aziyyar Sanata Rabiu Kwankwaso a Twitter

‘Dan siyasar ya yi wa masanin tattalin arzikin addu’a, tare da aika ta’aziyya ga ‘yanuwa da abokansa.

Innalillahi wa Inna Ilaihi Rajiun.

Ina mai takaicin rashin Farfesa Aminu Usman na jami’ar KASU kuma daya daga cikin ‘yan kwamitin yakin neman zaben shugaban kasarmu.

Allah ya yafe masa kura-kurensa. Ina mika ta’aziyyata ga damgi, abokai da abokan aikinsa.

– Sanata Rabiu Musa Kwankwaso

Daily Trust ta ce an birne Farfesa Usman ranar Lahadi a garin Zariya bayan an yi masa sallar jana’iza a masallacin Kofar Gayan da ke cikin garin.

Farfesan masani ne a kan tattalin arziki, shi ne shugaban kamfanin Al-amin Global Consult Ltd.

An yi rashin masanin tattalin arziki

Legit.ng Hausa ta fahimci Marigayin ya yi digirorin B. SC, M. Sc da PhD ne a ABU Zaria, Jami’ar Jos da NDA a shekarun 1988, 1993 da kuma 2012.

A lokacin rayuwarsa, ya yi rubuce-rubuce da bincike da-dama a kan sha’anin kudi, tashin kudin kasar waje da tsare-tsare da manufofin bankin CBN.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here