Me Kwankwaso da Obi ke Shirin ƙullawa?

 

A ranar Lahadi ne wasu manyan jiga-jigan hamayyar siyasar Najeriya suka kai wata ziyara ga jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, a gidansa, inda daga bisani aka gudanar da taro na siyasa da ɗaruruwan magoya baya suka halarta.

Cikin waɗanda suka kai ziyarar sun haɗa da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasar na jam’iyyar LP, Peter Obi da gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde da tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Sanata Seriake Dickson da sauransu.

Cikin wani saƙo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sanata Kwankwaso ya ce ƴan siyasar sun kai masa ziyarar gaisuwar sallah ne.

Dukkannin ƴan siyasar dai na cikin jam’iyyu mabanbanta juna, inda Kwankwaso ke jam’iyyar NNPP, shi kuma Peter Obi ke ADC sai kuma Seyi Makinde da Seriake Dickson da ke PDP.

Tambayar da jama’a ke yi dangane da taron ita ce shin me jiga-jigan ƴan siyasar suke ƙullawa a siyasance? Ko Kwankwaso zai koma jam’iyyar ADC mai hamayya? Sannan ko Peter Obi da Kwankwaso za su yi takara ne?

Me taron yake nufi?

Dr Kabiru Sufi, malami a kwalejin share fagen shiga jami’a a Kano ya ce taron da ya haɗa gaggan ƴan siyasar ba sabon abu ba ne amma kuma na wannan lokaci ya sha bambam da sauran.

“Lallai alamu na nuna cewa mutanen na da wani shiri na musamman dangane da yadda za a tunkari zaɓen 2027. Amma yanzu duk abin da wani zai ce sai dai hasashe. Amma taron ya ja hankali sannan ya sabunta batun haɗuwar Kwankwaso da ko Peter Obi ko Makinde”.

Kalubale biyu ga Peter da Kwankwaso

Dr Kabiru Sufi ya ce haɗuwar manyan ƴan siyasar na sabunta hasashen fitar da tikiti guda ɗaya sai dai kuma ya ce idan ma hakan ne to akwai ƙalubale guda biyu.

Wane ne shugaba, wane ne mataimaki?: Dr Sufi ya ce babban ƙalubale da tikitin Peter Obi da Kwankwaso zai fuskanta shi ne wane ne zai zama shugaban ƙasa sannan wane ne zai zama mataimaki.

A wace jam’iyya: A wace jam’iyya mutanen biyu za su tsaya takara? Idan a jam’iyyar ADC ne to akwai ƙalubale na tsohon mataimakin shugaban Najeriya, Atiku Abubakar wanda yake a jam’iyyar. Idan kuma jam’iyyar NDC za su yi to ya kamata su sauri su shiga domin gaggauta

aiwatar da komai saboda ka da lokaci ya ƙure musu.

Ko Kwankwaso zai yi wa Peter Obi mataimaki?

A 2024 an yi wa Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso irin wannan tambayar a cikin bidiyon mai tsawon kusan awa biyu.

A bidiyon an tambayi Rabi’u Kwankwaso kan ko zai karɓi muƙami a gwamnatin APC ƙarƙashin Tinubu. Tsohon sanatan na Kano ta Tsakiya ya ce ba zai karɓa ba duk da tayin da aka yi masa “a birnin Paris”.

Ya ci gaba da bayani har ya zo wurin da yake maganar tattaunawa da sauran jam’iyyu, ciki har da LP ta Peter Obi.

Na ce ni ba ni da matsala amma a kawo “criteria” [dalilin da zai sa na ajiye takara ta],” in ji shi. “Ba mu ne ba mu da ilimi ba ƴan Arewa? Ba mu ne kowa ya raina ba? Ni yayansa ne a siyasa.

“Kuma duk abin da aka ɗauko a saka a “criteria” [mizani] da ilimi. Ni ba sa’ana ba ne. Ni ina da PhD a “civil engineering” [harkokin gine-gine]. Riƙe muƙamai ba a fi ni ba. Ƙwazo na irin aikin da muka yi ma ba iri ɗaya ba ne a jiharsa da jihata.

“Na ce mene ne mizanin da zan yi masa mataimaki? Hankali dai ake amfani da shi ko? Kuma wannan jam’iyyar ai gina ta muke yi a hankali ko. Ba irin PDP ba ce da muka haɗu muka gina ta, ko kuma APC da kawai mutum zai shigo ya yi mata taka haye.

“Saboda haka mu muna nan muna jira, kuma a shirye muke mu tattauna da kowa. Amma duk abin da za a yi a yi shiri na gaskiya. Ka da a zo a faɗa min ƙarya.”

Wane tasiri Peter Obi da Kwankwaso za su yi?

“Ko da a ce sun haɗu [Kwankwaso da Peter Obi] in dai ba su shiga lungu da saƙo sun tallata manufofinsu ba to baza su yi wani tasiri ba,” in ji Farfesa Kamilu Fagge, masanin kimiyyar siyasa a Jami’ar Bayero da ke jihar ta Kano.

Ya ƙara da cewa “sannan sai sun haɗa ƙaƙƙarfar tawaga da za ta iya ja da jam’iyya mai mulki, saboda APC na da ƙarfin mulki.”

Masanin ya bayar da misali da tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, wanda ya shafe lokaci mai tsawo yana yi takara kuma yana samun ƙuri’u “amma bai iya cin zaɓen ba sai da ya nemo wani daga kudanci suka haɗa hannu”.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here