Tulin Kwarewa da na Samu ta Isa a ba ni Dama na Gaji Buhari a 2023 – Oshiomhole
Tsohon shugaban APC na ƙasa, Adams Oshiomhole, ya ce tulin kwarewar da ya samu ta isa a ba shi dama ya gaji Buhari a 2023.
Oshiomhole, wanda ya ayyana tsayawa takarar Sanata, ya ce ya gano cewa kujerar shugaban ƙasa ce ta dace da shi a Najeriya.
Ya kuma yi bayanin yadda za’a kawo ƙarshen yajin aikin kungiyar Malaman jami’o’i ta ƙasa ASUU.
Abuja – Tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Kwamaret Adams Oshiomhole, ya bayyana dalilin da yasa ya cancanci a zaɓe shi shugaban kasa a 2023 a Najeriya.
Read Also:
Tsohon gwamnan jihar Edo ya ce yana da kwarewa a fannoni daban-daban na rayuwa, da suka haɗa da ƙungiyanci da hukumomi masu ƙalubale, kamar yadda Daily Trust ta rahoto.
Kwamaret Oshiomhole ya yi wannan jawabin ne a shirin Labaran Arise ranar Laraba lokacin da yake tsokaci kan nufinsa na tsayawa takarar shugaban ƙasa.
Tsohon shugaban jam’iyya mai mulkin ya ce:
“Idan kuka duba tushe na, na tsallake kowane irin siraɗi, na yi aiki a karamin mataki, na kai kololuwa a ma’aikata, an jarabce ni da mulki a tattalin arziki, muƙamin siyasa, na yaƙi masu mulki da bincike su.”
“Bayan haka na zama gwamnan jihar Edo inda na yi koƙarin aiwatar da wasu abubuwa da na jima ina faɗa lokacin ina ƙungiyar Kwadugo NLC.”