Zaɓen Edo: Ina Cike da ƙwarin Gwiwa a Wannan Zaɓe – Ɗan Takara LP

 

A nasa ɓangare ɗan takarar jam’iyyar LP a zaɓen gwaman jihar Edo, Olumide Akpata ya ce yana cike da ƙwarin gwiwar samaun nasara a zaɓen da ke gudana a jihar.

Yayin da yake magana da yake hira da wakilan gidan talbijin na Arise TV jim kaɗan bayan kaɗa ƙauri’arsa, Mista Akpata ya ce ya ji ɗaɗin yadda mutane suka fito zaɓen.

Ya kuma ƙara da cewa alamu sun nuna cewa zaɓe na tafiya yadda ya kamata, kuma yana kan hanyar samun nasara.

”Na ji daɗin yadda mutane suka fito zaɓen, kuma hakan alamu ne da ke nuna cewa mutane na cike da fatan samun chanji”, in ji shi.

”A ganina komai na tafiya yadda ya dace zuwa yanzu, kuma ina fatan haka yake a faɗin jihar Edo”.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here