Hukumar Kwastam ta Kama Kwantena Dauke da Makamai a Jahar Legas

Hukumar Kwastam a Najeriya ta ce ta kama wata kwantena maƙare da makamai a Tin Can Island da ke Jahar Legas ranar Juma’a.

A cewar hukumar, mamallakin kwantenar ya bayyana cewa akwatinan talabijin ne a ciki kafin daga bisani a gano bindigogi da kuma harsasai a ciki.

Wata sanarwa da kakakin hukumar ya fitar ranar Asabar ta ce an kama makaman ne yayin da jami’anta ke sintirin duba kayayyaki kamar yadda aka saba, inda nan take aka mayar da kayan wurin duba kayayyaki.

“Jami’ai sun kama wata kwantena cike da makamai, abin da muka yi a matsayinmu na hukuma shi ne mun rubuta wa tashar cewa a yi gaggawar ɗauke kayan zuwa wurin duba kayayyaki a nitse saboda mu bincika su da zimmar gano sauran bayanai,” in ji Uche Ejesieme.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here