Kwastam ta Kama Kwantenoni 20 ɗauke da Lalatacen Tumatir
Hukumar kwastam a Najeriya ta ce ta kama duro 1,600 na tumatir ɗin da ya lalace wanda aka sanya cikin wasu kwantenoni guda 20 a jihar Legas.
An kama kwantenonin ne a tashar jiragen ruwan Legas, tare kuma da cafke wani mutum guda da ake zargi da shigo da su.
A cewar shugaban hukumar ta kwastam, Adewale Bashir, ya ce ana zargin kwantenonin mallakin wani kamfani ne mai suna Nikecristy Investment Limited.
Read Also:
Ya ce jami’ansu ne da ke sintiri ne suka samu nasarar kama kwantenonin guda 20, waɗanda daga bisani aka gano cewa suna ɗauke da tumatirin da ya lalace, wnada kuma zai yi wa mutane illa idan suka yi amfani da shi.
Ya ƙara da cewa kwantenonin da aka shigo da su daga ƙasar Sifaniya, za a biya musu kuɗin fito naira miliyan 116.2
“Abin Alla-wadai ne yadda waɗannan mutanen suka shigo da waɗannan kayayyaki da suka lalace zuwa cikin kasuwannin Najeriya,” in ji Adewale.
Ya ce zuwa yanzu kwantenonin na karkashin kulawarsu har sai bayan an kammala bincike.