Hukumar Kwastam ta Kama Motoci 13, Buhuhunan Shinkafa 314 a Jahar Katsina

 

Hukumar Kwastam tayi babban kamu da jahar Kastina.

Har yanzu gwamnatin Buhari ta haramta shigo da shinkafa yar waje.

Hukumar ta ce ta gano wasu dabarun da masu fasa kwabri keyi wajen shigo da kaya.

Hukumar Kwatsam ta sanar da cewa ta damke motoci 13, buhuhunan Shinkafa 314 da wasu kayayyaki da kudin dutinsu ya kai milyan 60 a jahar Katsina.

Hukumar ta yi wannan kamu ne cikin wata guda tsakanin ranar 8 Yuli da 3 ga Agusta. Mukaddashin Kontrolan Kwastam na jahar Katsina, Dalha Wada, ya bayyana hakan ranar Talata a Kaduna yayin hira da manema labarai kan nasarorin da yankinsa ta samu, Punch ta ruwaito.

A cewar Wada, a cikin wata guda, hukumar ta kama motar kirar Lexus 2011, da Toyota Corolla 2015.

Wada yace:

“Hukumar ta damke manyan buhuhunan Shinkafa 314 mai kimanin kudi N7.5m, galolin man gyada 25ltr guda 227 mai kimanin kudin N715,000 da katon na taliyar waje 178 mai kimanin kudi N961,000.”

Wada ya kara da cewa sun damke Dabino mai kumanin kudi N2.2m, da waken Soya na kimanin kudi N262,000.

A cewarsa, hukumar na iyakan kokarinta wajen hana masu fasa kwabri shigowa Najeriya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here