Hukumar kwastam ta Kwace Haramtattun Kayayyaki da Darajarsu ta kai N41.4m a Jahar Kano

 

Hukumar Kwastam ta Najeriya ta kama buhu 707 na shinkafar waje da aka yi fasakwaurin ta a Jahar Kano.

Ofishin Hukumar reshen Jigawa da Kano ya ce sun kwace shinkafar ne tare da wasu kayayyakin da aka yi fasakwaurinsu.

Kimar kudaden kayan da suka kama ta kai Naira miliyan 41.3 daga watan Yuli zuwa Satumba.

Hukumar kwastam ta kwace haramtattun kayayyaki da darajarsu ta kai Naira miliyan 41.4 a jahar Kano da Jigawa a cikin watanni ukun da suka gabata.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa kwanturolan hukumar na shiyar Kano da Jigawa, Suleiman Pai Umar, ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, 23 ga watan Satumba.

Rabe-raben abubuwan da aka kwace sun haɗa da: buhuhunan shinkafa yar waje 707 wadanda kimar kudadensu ya kai N20.5 miliyan, dila 155 na kayan gwanjo na N11.6 miliyan, jarkoki 625,16 na man girki kan N334,000, kwalayen taliya 130 na N1.95 miliyan, kwalayen madara 231 na N5.08 miliyan da kwalin macaroni takwas na N104,000.

Sauran abubuwan da aka kama sun hada da: kwali 30 na maganin sauro na hayaki na N660,000, katan 29 na Couscous da kudinsa kai N337,000, katan 10 na batir na N220,000, katon shida na angur da aka sarrafa a kasar Ghana na N308,000 da katan 85 na magungunan da ba a yi wa rajista ba.

Umar ya nuna damuwa cewa har yanzu wasu ‘yan Najeriya na ci gaba da yin fasa kwauri duk da sanin barazanar fasa-kwaurin ga lamarin tsaro da tattalin arzikin ƙasar, jaridar Punch ta rawaito.

Ya ce:

“Kamen wani bangare ne na ayyukanmu na hana fasa kwauri tun daga watan Yuli. Yana da ban tsoro cewa har yanzu wasu ‘yan Najeriya na ci gaba da yin fasa kwauri, duk kuwa da yawan sanin barazanar fasa kwauri ga tsaro da tattalin arzikin kasar.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here