Jami’an Hukumar Kwastam Sun Kwato Buhuhunan Shinkafa a Jahar Oyo

 

Jami’an hukumar kwastam sun dira kasuwar Oja Oba dake Ibadan, babban birnin jahar Oyo inda suka yi awon gaba da buhuhunan shinkafa.

Kakakin hukumar kwastam ɗin na Sakta A, ya tabbatar da faruwar lamarin amma yace baisan adadin buhunan da aka ƙwato ba.

Yace dokar hukumar su ta baiwa jami’ai damar ɓalle kowane irin shago ko babban ɗakin ajiye kaya matuƙar akwai sahihin bayani cewa an ajiye haramtattun kaya a cikinsa.

Jami’an hukumar kula da shige da ficen kaya (NCS) sun dira kasuwar Oja Oba dake Ibadan da sanyin safiyar ranar Asabar inda suka yi awon gaba da motar ɗaukan kaya maƙare da buhunan shinkafa yar ƙasar waje.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, wannan na zuwa ne wata ɗaya bayan jami’an sun kai irin wannan samamen a kasuwar Bodija, inda a wancan lokacin suka yi awon gaba da buhunan shinkafa.

Kakakin hukumar kwastam na sakta A, Mr Theophilus Duniya, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata hira da akai dashi ta wayar salula.

Theophilus Duniya, ya bayyana cewa aikin su ya basu ikon ɓalle kowane shago ko babban ɗakin aje kaya matukar suna zargin an ajiye haramtattun kaya a ciki.

Yace: “Kwarai mun gudanar da aiki a wannan kasuwar, amma bazan iya faɗa muku adadin buhunan shinkafar da muka kama ba a yanzun haka.”

“A iya abinda nasani, bayan gudanar da irin wannan aikin, ana ƙirga yawan buhuhunan shinkafar da aka kamo. Amma a yanzun da nike magana bazan iya faɗa muku sakamakon wannan aikin ba, tabbas jami’an mu sunje wannan kasuwar kuma sun kwato shinkafa.”

“A dokokin hukumar mu NCS, an ba jami’ai damar su ɓalle kowanne shago ko babban ɗakin aje kaya matuƙar suna da sahihin bayanai cewa an ajiye haramtattun kaya a cikinsa.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here