Hukumar Kwastam ta ƙasa ta Samar da Kimanin N799bn a Cikin Watanni Biyar

 

Hukumar kwastam ta ƙasa ƙarƙashin jagorancin Hameed Ali ta kafa sabon tarihi na samar da kuɗin shiga ga gwamnati.

A karo na farko NCS ta samar da kuɗaɗen shiga kimanin biliyan N799bn a cikin watanni biyar kacal.

Kakakin hukumar kwastam na ƙasa, Joseph Attah, shine ya bayyana haka ga manema labarai a Abuja.

Hukumar kwastam ta ƙasa (NCS) ta samar da kuɗi kimanin biliyan N799bn na kuɗaɗen shiga daga watan Janairu zuwa Mayu 2021, karon farko a tarihin hukumar, kamar yadda Daily Nigerian ta ruwaito.

Kakakin NCS, Joseph Attah, shine ya bayyana haka ga manema labarai a babban birnin tarayya Abuja.

Mr Attah yace wannan adadin ya zarce abinda hukumar ta samar a irin wannan lokacin a shekarar data gabata 2020.

Ya ƙara da cewa hukumar ta samu wannan nasara ne saboda zartad da dukkan wata doka ta shige da ficen kayayyaki a fadin ƙasar nan.

Attah yace dabarun canza wa jami’an hukumar wurin aiki da kuma cigaba da yin hakan na ɗaya daga cikin dalilan da yasa hukumar ta cimma wannan nasara.

A cewarsa, ƙara wa jami’an NCS ƙarfin guiwa su saka ƙasar su a gaba fiye da buƙatunsu na daga cikin abinda yasa kuɗaɗen shigan suka ƙaru.

Yace wasu dalilan sun haɗa da, ƙarin samun haɗin kai da aka samu daga masu faɗa aji na ƙasar nan da kuma kyakkyawar alaƙa tsakanin NCS da yan majalisun ƙasar nan.

Kakakin NCS ɗin ya ƙara da cewa: “Hukumar kwastam ƙarƙashin jagorancin Hameed Ali zata cigaba da ɓullo da sabbin dabaru waɗanda zasu taka muhimmiyar rawa wajen farfaɗo da tattalin arziƙi da tsaro.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here