Abba Kyari ba Zai Shiga Amurka ba Har Sai Kotu ta Yanke Hukunci – Ministan Shari’a
Ministan shari’a, Abubakar Malami ya tabo batun zargin da ke kan Abba Kyari.
Abubakar Malami ya ce akwai yarjejeniya tsakanin kasar Amurka da Najeriya.
Minista ya ce Abba Kyari ba zai shiga Amurka ba har sai kotu ta yanke hukunci
Abuja – Ministan shari’a na Najeriya, Abubakar Malami SAN, ya yi magana game da zargin da ake jifan babban jami’in ‘dan sanda, Abba Kyari da shi.
Dokar kasa za ta yi aiki a kan Abba Kyari Legit.ng ta samu labari Abubakar Malami ya ce dokar kasa ce za ta yi aiki wajen hukunta Abba Kyari.
Ministan ya bayyana wannan ne lokacin da aka yi wata hira da shi a gidan rediyon Voice Of America (VOA) a ranar Alhamis, 5 ga watan Agusta, 2021.
Akwai yarjejeniya tsakanin Najeriya da Amurka?
Abubakar Malami yake cewa duk da akwai yarjejeniya tsakanin gwamnatin tarayya da kasar Amurka, za a bar doka ta yi aiki sarai wajen hukunta Kyari.
“Eh, akwai yarjejeniya tsakanin Najeriya da Amurka a kan taso keyar duk wanda aka samu ya aikta laifi a cikin kasashen; Amrka ko Najeriya.”
Read Also:
Babban lauyan gwamnatin tarayya ya ce hukuncin da kotu ta yanke shi ne zai yi tasiri wajen mika jami’in tsaron ga hukumomin Amurka da ke tuhumarsa.
“Amma akwai sharuda, sharudan su ne duk lokacin da kasa ta rubuta wa ma’aikatar kasar waje, ma’aikatar za ta aika wa ministan shari’ar shari’a takara domin kotu ta bada dama a dauke wanda ake zargi ya tafi Amurka, domin ya amsa tambayoyi.”
“Ba na cewa za a damka Abba Kyari ga masu neman shi, amma doka za ta yi aiki da kyau kafin a dauki wani mataki.”
Jaridar The Nigerian Lawyer ta rahoto Ministan shari’an ya na cewa sai Alkalai sun bada dama sannan Kyari zai tafi Amurka ya amsa zargin da ke wuyansa.
Da wannan matsaya da Mai girma Ministan ya dauka, ya nuna gwamnatin Muhammadu Buhari ba ta zabi bangare a shari’ar Ramon Azeez watau Huspuppi ba.
An dakatar da Kyari
daga aiki A baya an ji labari cewa Hukumar da ke kula da ayyukan ‘yan sanda ta kasa, PSC ta dakatar da Abba Kyari kan zarginsa da hannu a badakalar Hushpuppi da FBI.
Dakatarwar DCP Kyari ta fara aiki ne daga ranar Asabar, 31 ga Yuli, 2021, kuma za a ci gaba da sauraron sakamakon binciken da kwamitin da aka nada yake yi.