Mutanen NNPC Sun Buɗe Kamfanin Tace Mai a Malta: Kyari ya Mayar wa Dangote Martani
Shugaban kamfanin NNPC Mele Kyari ya mayar wa attajirin Afirka Aliko Dangote martani bayan zargin cewa wasu mutanen NNPC sun mallaka kamfanin tace mai a ƙasashen ƙetare.
A sanarwar da ya wallafa a shafinsa na X, Mele Kyari ya yi watsi da zargin inda ya ce ba shi da wani kamfani na tace mai a ƙasashen ƙetare.
A wani bidiyo da ke yawo a kafofin sada zumunta, Aliko Dangote ya yi zargin cewa wasu ƴankasuwar mai da mutanen NNPC sun buɗe kamfanin tace mai a Malta.
“Mun san inda ake wannan aikin kuma mun san me suke yi, ba wai ba mu sani ba,” in ji Dangote.
Read Also:
Da yake mayar da martani, Shugaban NNPC ya ce “ba ni da wani kasuwanci ko wanda ake yi da sunana a ko’ina a duniya idan ba wanda nake yi ba gida na aikin gona.”
“Sanna ba ni da masaniya ko akwai ma’aikacin NNPC da yake da matata a Malta ko wani wuri a sassan duniya.”
Shugaban na NNPC ya buƙaci a fallasa waɗanda Dangote yake zargi tare da sanar da jami’an tsaro domin ɗaukar matakin da ya dace da su.
A cikin bidiyon da ke yawo na Dangote, ya yi zargin ana shigo da man da ba ya da inganci a Najeriya, dalilin ya sa wasu ke samun matsaloli a motocinsu, a cewarsa.
Ya ce idan har ana son tabbatar da gaskiyar abin da yake fada – abin da ya kamata a gudanar shi ne gwaji kan man da ake sayarwa a gidajen mai amma ba daga tashar ruwa ba.
“Wani kawai zai shigo da jirgin ruwa ya gabatar da samfuri da takardar bogi sai a sahale masa – nan gaba za mu ci gaba da magana,” in ji Dangote.