Ministan Yada Labarai da Al’adu, Lai Mohammed Yaja Kunnan ‘Yan Bindiga

 

Lai Mohammed ya bayyana cewa, ana kokarin sanyawa ‘yan Najeriya tsoro ne kawai a kasar.

Ya kuma bayyana cewa, gwamnatin tarayya da na isasshen karfin ragargazar ‘yan bindiga.

Hakazalika ya bayyana yadda wasu bata-gari ke son ingiza kasar cikin halin rashin tsaro.

Lai Mohammed, Ministan yada labarai da al’adu, ya ce ‘yan bindigar da ke addabar kasar za su dandana kudarsu, TheCable ta ruwaito.

An samu matsalar yawaitar barnar ‘yan bindiga a duk fadin kasar wadanda suka kai ga satar mutane tare da neman kudin fansa da kuma aikata fashi da makami.

Da yake jawabi a taron manema labarai a Legas a ranar Talata, Mohammed yace jami’an tsaron kasar sun fuskanci hare-hare na “rashin tunani” daga ‘yan bindiga don cusa tsoro da haifar da rashin tsaro.

Ministan ya ce sabanin ra’ayin wasu ‘yan kasar, gwamnatin tarayya ba ta dulmuye ba saboda kalubalen tsaro.

“Ina so in fada, ba tare da wata shakka ba, cewa duk wani hari kan jami’an tsaronmu maza da mata, hari ne kan kasar da kuma shelar yaki da al’ummar kasar,” “Akan yi haka ne, saboda, a dulmuya karfin hukumomin tsaro.

Yayin da wadanda suke da alhakin kare mu su kansu suke fuskantar hare-hare marasa tunani, hakan na faruwa ne saboda dalili daya kawai; Don cusa tsoro da haifar da rashin tsaro a tsakanin mutane.

“Ko sanannu ne ko ba a san su ba, wadanda ke aikata wannan mummunan aikin za su dandana kudarsu.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here