Cibiyar Arewa: Gwamna Lalong Zai Gudanar da Lakca Karkashin Jagorancin Tinubu

 

Jagoran APC kuma tsohon gwamnan jahar Lagos, Bola Ahmed Tinubu zai jagoranci gudanar da lakcar cibiyar Arewa wato ‘Arewa House’ da aka saba yi duk shekara.

Daractan Arewa House, Dr Shuaib Aliyu ne ya sanar da haka ga manema labarai a Kaduna.

Haka zalika an bayyana gwamnan jahar Plateu, Lalong a matsayin wanda zai gudanar da Lakca a wajen taron.

Jagoran jam’iyyar APC na kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu zai shugabanci lakcar da za’a gudanar a cibiyar Arewa karo na 11 a ranar Asabar.

Daraktan wurin, Dr Shuaibu Shehu Aliyu ya fada ma yan jarida a Kaduna ranar Alhamis, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.

Yace lakcar karshe wato ta 10, wadda gwamnan babban bankin Najeriya na wancan lokacin, Sanusi Lamido Sanusi, ya gabatar kuma Oba na Lagos Oba Rilwan Akiolu ya shugabanta.

A yanda yace, An lura sosai wajen zabar Tinubu da Lalong domin jagorantar lakcar.

A cewarsa: “Ina mai farin cikin sanar daku cewa gwamnan jahar Filato Simon Bako Lalong zai gudanar da lakcar wannan shekarar a karkashin jagorancin Asiwaju Bola Ahmed Tinubu a ranar 27 ga watan Maris na 2021.” akcar wacce aka shirya ta musamman domin wayar da kai kan hadin kan kasa.

An zabi gwamna Lalong ne duba da cewa shine shugaban gwamnonin Arewa da kuma kwarewar sa wajen jagorantar jahar Filato.

Ana ma gwamnan kallon ya zayyi da rikice-rikicen jahar na tsawon shekaru 20 baya. Amma daga hawan sa mulki ya samu ya kawo karshen wadannan rikice-rikicen.

“Haka kuma dangane da shugabanci, a koda yaushe muna duba ayyukan da muhimman mutane sukayi kafin mu zabi wanda zai shugabanci lakcar. Asiwaju Bola Tinubu an zabe shi domin ya kara ma taron armashi da kuma kawo cigaba da hadin kan kasa” inji Daraktan.

Ya bayyana cewa lakcar shekara-shekara ta cibiyar Arewa wato ‘Arewa House’ ta kasance ana gudanar da ita tun shekarar 1994.

Kuma lakcar ta kunshi kowa da kowa ba tare da duba da kabila, addini ko kuma siyasa ba.

A na dai gabatar da lakcar ne domin girmama tsohon Firimiyan Arewacin Najeriya, Sir Ahmadu Bello Sardaunan Sokoto.

Gwamna Lalong zai yi magana ne akan ‘yadda za’a rage yawan kashe kuɗi a gwamnati da kuma sanya matasa wajen kawo cigaban kasa bayan annobar Korona.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here