Lamarin Buhari da Ban Tausayi Saboda Munanan Abubuwa na Faruwa a Gabanshi Amma ba Zai Iya Komai ba – Buba Galadima
Sakataren kwamitin amintattun jam’iyyar NNPP ya yi kira da yan Najeriya suyi addu’a Buhari ya karasa wa’adinsa ya tafi lafiya.
Alhaji Buba Galadima ya bayyana cewa a gaban Buhari aka abubuwan da basu dace amma bai iya komai.
Buba Galadima ya kasance kakakin kamfen Atiku a PDP a 2019 amma yanzu ya koma jam’iyyar NNPP.
Birnin Kebbi – Tsohon na kusa da Shugaba Muhammadu Buhari, Injiniya Buba Galadima, ya siffanta gwamnatin APC a matsayin mafi lalaci a tarihin Najeriya.
Read Also:
Vanguard tace Buba Galadima ya bayyana mata hakan ne a hirar da yayi a Birnin Kebbi inda dan takarar jam’iyyar New Nigeria Peoples Party, Rabiu Musa Kwankwaso, ya kai ziyara.
Galadima yace lamarin Buhari da ban tausayi saboda munanan abubuwa na faruwa a gabanshi amma ba zai iya komai ba.
Yace a wa’adin Buhari na farko, sun yi tunanin yan Najeriya basu fahimceshi bane, amma duk ya kunyatasu.
Yace:
“Addu’ata daya yanzu kuma ina kira ga yan Najeriya suyi shine ya samu ya karasa mulkinsa cikin lafiya, saboda gwamnatinsa za ta zama mafi muni a tarihin Najeriya.”
Game da yakin neman zabe kuwa, Buba Galadima, wanda shine sakataren kwamitin amintattun jam’iyyar yace NNPP da zama zakaran gwajin dafi a Najeriya yanzu.
Yace yadda suke samun kyakkyawan tarba daga wajen yan Najeriya a ziyarce-ziyarcen da suke kaiwa Arewa da Kudu, yana da tabbacin Kwankwaso zai yi nasara a 2023.