Zargin Gwamnatin Buhari da Yin Sake da Lamarin Tsaro: Lai Mohammed ya Mai da wa Jam’iyyar PDP Martani
Lai Mohammed ya mai da martani kan jam’iyyar PDP dake zargin gwamnatin Buhari da yin sake da lamarin tsaro.
Ya bayyana cewa, ba laifin gwamnatin tarayya bane halin da ake ciki, laifi ne na gwamnatocin jahohi ciki har da na PDP.
Ya kuma caccaki taron manema labarai da jam’iyya da cewa ba komai bane taron face wasa kawai da suka shirya.
Ministan Yada Labarai, Lai Mohammed ya nemi jam’iyyar PDP da ta ga laifin gwamnatocin jahohi, ciki har da wadanda mambobin jam’iyyar ke shugabanta, a kabubalen tsaro da kasar ke fuskanta.
Read Also:
A cewarsa, bindiganci da ta’addancin masu satar mutane ba laifin gwamnatin tarayya bane, Channels Tv ta ruwaito.
Shugabannin PDP sun yi taron manema labarai a ranar Litinin, inda suka nuna rashin amincewarsu kan irin halin rashin tsaro da ake ciki a kasar tare da neman gwamnatin tarayya ta magance matsalolin gaba daya.
Mista Mohammed, memba ne na jam’iyya mai mulki ta APC, ya ce abin takaici ne yadda jam’iyyar adawa ba ta fahimci kokarin da wannan gwamnati mai ci ke yi a kan lamarin ba ciki har da taron zauren garin da aka gudanar a Kaduna inda aka tsara wani shiri na matakai goma.
Ya ce taron manema labarai na PDP ba komai bane face wasa kawai kuma ya kara zargin jam’iyyar da kokarin siyasantar da batutuwan da suka shafi tsaron kasa.