Mustapha Sule Lamido ya Lashe Tikitin Takarar Gwamna a Jihar Jigawa
Kamar mahaifinsa, Mustapha Lamido ya tsallake matakin farko na zama gwamnan jihar Jigawa.
Dan tsohon gwamnan ya lashe zaben fidda gwanin jam’iyyar adawa ta jihar, Peoples Democratic Party PDP.
Mustapha Lamido ya yi kira ga mambobin jam’iyyar su bashi hadin kai don samun nasara a zabe.
Dutse – Mustapha Lamido, dan tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido, ya lashe zaben fidda gwanin yan takarar gwamnan a Jigawa na jam’iyyar Peoples Democratic Party, PDP.
Baturen zaben fidda gwanin, Isah Ahmed, ya bayyana hakan lokacin ya sanar da sakamakon zaben ranar Laraba a Dutse, rahoton Daily Nigerian.
Read Also:
Isah Ahmed ya sanar da cewa Mustapha Lamido ya samu kuri’u 829 cikin mutum 832 da suka ka’da kuri’a yayinda abokin hamayyarsa Saleh Shehu bai samu kuri’a ko guda ba.
Mustapha ya bayyana farin cikinsa bisa wannan nasara kuma ya yi kira ga yan jam’iyyar su bashi amanar gyara jihar Jigawa idan suka samu nasara.
Yace:
“Ina kira ga ku nisanci siyasar rabuwar kai. Jihar nan ta fi kowannenmu. Yayinda mukzamu shiga mataki na gaba na kamfe da zabe, ina kira ga ku yarda da ni, kuyi aiki dani, kuyi min kamfe kuma ku zabe ni saboda mu gyara jihar.”
Shugaban jam’iyyar PDP na jihar, Babandi Ibrahim, a jawabinsa ya bayyana cewa jam’iyyar zatayi iyakan kokarinta wajen lashe zaben gwamnan jihar.