Lauya ya Shigar da Karar INEC a Kotu kan Takardun Takarar Tinubu
Barista Mike Enahoro-Ebah zai yi shari’a da hukumar zabe na kasa mai zaman kanta watau INEC.
Lauyan ya yi amfani da FOI, ya nemi INEC ta damka masu duk wasu takardun takarar Bola Tinubu.
Ganin har yanzu bai samu biyan bukata ba, Mike Enahoro-Ebah ya nemi kotu ta tursasa INEC.
Abuja – Mike Enahoro-Ebah, wanda kwararren Lauya ne a Abuja ya shigar da karar hukumar INEC a kotu a game da takardun takarar Asiwaju Bola Tinubu.
Daily Trust ta kawo rahoto a ranar Lahadi, 7 ga watan Agusta 2022 cewa Lauyan ya kai karar ne domin INEC ta fitar da takardun CTC na ‘dan takaran na APC.
Mike Enahoro-Ebah ya kuma nemi kotu ta umarci hukumar zabe na kasa watau INEC ta fitar da takardun shiga takara a 1999 da 2003 da Tinubu ya gabatar.
‘Dan siyasan ya yi takarar kujerar gwamna a zaben 1999 da na 2003, ya kuma yi nasarar zarcewa a kan kujerar gwamnan jihar Legas a karkashin jam’iyyar AD.
Read Also:
A halin yanzu Bola Tinubu yana neman takarar kujerar shugaban kasa a jam’iyyar APC mai mulki.
Lauyan ya shigar da kara mai lamba FHC/ABJ/CS/1337/2022 a babban kotun tarayya, yana so INEC ta mallaka masa takardun EC 13A da EC 9 na Bola Tinubu.
Haka zalika Mike Enahoro-Ebah ya bukaci Alkali ya ba shi damar ganin takardun da Bola Tinubu ya mikawa INEC kafin ya shiga takarar gwamna a jihar Legas.
Lauya ya yi amfani da FoI
A cewar Lauyan, ya bukaci INEC da wannan bukata a watan Yuli, yana mai dogara da dokar FOI ta 2011. FOI ta ba ‘dan kasa samun duk bayanan da yake nema.
Abin da dokar tace shi ne idan mutum ya nemi samun bayanai, zai jira na tsawon makonni biyu, bayan nan zai iya neman kotu ta sa baki idan har ya ji shiru.
Idan aka yi la’akari da sashe 29(4) na dokar zabe da dokar FOI ta kasa, Enahoro-Ebah yace an aikata laifi idan aka boyewa Duniya takardun ‘dan takaran na APC.
Ba mu da labari ko kotun da ke zama a Abuja ta sa ranar da za a fara sauraron wannan shari’a.