Legas: Wasu Dalibai Sun Kamu da Cutar Korona

Annobar COVID-19 tana cigaba da yaduwa a jihohi kamar Legas, musamman bayan bude makarantu.

An samu wasu malamai 5 da dalibi daya da ke dauke da cutar a wata makarantar sakandare.

Bayan wata malama ta fadi ciwo a makarantar da ke jihar Legas aka gano sauran masu cutar Wasu malamai 5 da dalibi daya, sun kamu da cutar COVID-19 a wata makarantar sakandare da ke jihar Legas.

Gwamnatin jihar Legas ta sanar da hakan a ranar juma’a, jaridar The Punch ta wallafa.

Kamar yadda takardar mai taken jihar Legas ta tabbatar da samun wasu masu cutar COVID-19 a wata makarantar sakandare kuma kwamishinan lafiya, Farfesa Akin Abayomi ya tabbatar da hakan.

Wani bangare daga cikin takardar yazo, “Gwamnatin jihar Legas ta tabbatar da kamuwar wasu da cutar COVID-19 a wata makarantar sakandare ta kwana da ke mainland.

“An samu wata malamar makarantar mai dauke da cutar COVID-19 a ranar 2 ga watan Nuwamba.

“Bayan an bi diddiki, an gano wani dalibi da wasu malamai 4 da ke dauke da cutar.

“Bayan daya daga cikin malaman ya fadi ciwo na wasu ‘yan kwanaki, an kai shi asibitin makarantar, inda aka fara kula da lafiyarsa.

Da aka yi wa malaman gwajin COVID-19 sai aka gano suna dauke da cutar a ranar Litinin, 2 ga watan Nuwamba.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here