‘Yan Karamar Hukumar Madagali da ke Adamawa Sun Koka da Rashin Tsaro

 

Jama’ar karamar hukumar Madagali da ke jihar Adamawa sun koka a kan harin da Boko Haram ke kai musu.

A cikin kwanakin nan, mayakan ta’addancin da ke zama a dajikan yankin sun sace masu mata hudu.

Sun sako daya daga cikin matan ganin matar aure ce kuma a cewarsu ta yi musu tsufa don haka bata da abun mora.

Mazauna karamar hukumar Madagali ta jihar Adamawa sun yi kira ga gwamnati da ta inganta tsaro bayan sace ‘yan mata uku da mayakan Boko Haram suka yi.

Madagali tana daya daga cikin kananan hukumomi bakwai da mayakan Boko Haram suka kwace a 2014 kafin sojin Najeriya su kwato su a 2015, Daily Trust ta ruwaito.

Mazauna yankin sun bayyana cewa ‘yan mata biyu tare da matar aure daya ne ke aiki a gona a makon da ya gabata a wani kauyen Dar yayin da wasu mutane dauke da makamai suka cafkesu.

Daga bisani sun saki matar auren saboda sun ce ta yi musu tsufa.

“Har yanzu ‘yan matanmu na hannunsu tun sace su da suka yi a makon da ya gabata. Muna kira ga gwamnati da dakarun soji da su yi duk abinda ya dace wurin ceto su,” wani mazaunin yankin ya sanar.

Wani mazaunin yankin har ila yau mai suna Iskarju Ezekiel ya yi kira ga hukumomin tsaro da su taimaka wurin kakkabo ‘yan Boko Haram da ke da maboya a kewayen Madagali da sauran yankunan Borno.

“Abubuwan na faruwa kadan-kadan saboda akwai ragowar ‘yan Boko Haram a dajikan da ke zagaye da mu. Muna rayuwa cikin tsoro ballantana da suka sace ‘yan mata a ranar Litinin,” yace.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here