Nayi Mafarki Akan Cewa Zan yi Kudi Idan Har na Shafa Jinin ‘Dana a Kaina – Magidancin da ya Kashe ‘dan sa

 

Wani magidanci mai suna Mista Volt Blessing Gabriel, dan shekaru 33 ya shiga hannun yan sanda a jihar Delta bisa zargin kashe dan cikinsa.

Gabriel dai ya ce ya yi mafarki da wani mutum ne idan ya fada masa cewa zai yi kudi idan har ya shafa jinin dan nasa a kansa.

Tun farko dai mahaifiyar yaron ce ta kai karar mijin nata ofishin yan sanda bayan ta gaza ganin dan nata sannan mai gidan nata ya yi mata yawo da hankali.

Delta – Jami’an yan sandan jihar Delta sun kama wani mutum mai shekaru 33, Mista Volt Blessing Gabriel, kan amfani da zarto wajen sare kan dansa mai shekara daya don yin asirin kudi.

Gabriel wanda ya kashe dan nasa mai suna Godspower a jeji a garin Benin, jihar Edo, ya binne kan mamacin a kusa da wata bishiyar kwakwa sannan ya jefar da gawar, jaridar Vanguard ta rahoto.

An tattaro cewa mai laifin ya ce ya kashe yaron ne saboda ya yi mafarki cewa idan ya aikata hakan, sannan ya shafe kansa da jinin, zai yi arziki.

Kakakin yan sandan jihar Delta, Mista Bright Edafe, wanda ya tabbatar da lamarin a cikin wata sanarwa, ya ce an kama Gabriel ne bayan matarsa ta gano batan dan nata sannan ta kai rahoton cewa tana zargin mijin nata.

“A ranar 25/06/2022, da misalin karfe 10:30, wata Misis Success Oduwa mai shekaru 24 a mararrabar Peanuts, Obeh a jihar Edo, ta gano cewa bata ga danta ba tun da safiyar 24/06/2022 sannan sai ta fara damun mijinta kan ina danta yake.

“Mijin nata ya sanar da ita cewa dan na tare da yar’uwarsa a Warri. Da isarta Warri, sai ta gano cewa mijin nata karya ya yi mata, don haka sai ta fara zarginsa.

“Sai ta kai rahoton lamarin ga kwamandan RRS, cewa tana zargin mijinta mai suna Volt Blessing Gabriel mai shekaru 33, wanda ke a adireshi daya da ita ya kashe masu dansu mai suna Godspower Gabriel, mai shekara daya da wata takwas a duniya don kudin asiri.

“Sai kwamandan RRS ya ba jami’ansa bayani, inda suka shiga aiki, suka kama mijin sannan suka mika shi ga DPO na sashin ‘A’ Division Warri don ci gaba da bincike.

“Da ake masa tambayoyi, sai wanda ake zargin ya ce shi ya kashe dan a jejin Ewabogun hanyar katolika, birnin Benin, ta hanyar amfani da zarto wajen fille masa kai sannan ya binne shi a kusa da wata bishiyar kwakwa da ke dajin ya kuma jefar da gawar yaron mara kai.

“Wanda ake zargin ya kuma bayyana cewa ya kashe yaron ne saboda yayi mafarki, inda ya ga wani mutum wanda ya fada masa cewa idan ya kashe yaron sannan ya goga jininsa a kansa, zai zama mai kudi. Wanda ake zargin yana tsare.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here