Gwamna Yahaya Bello ne Zai Iya Zama Magajin Shugaba Buhari – Sanata Smart Adeyemi
Sanatan jam’iyyar APC daga jahar Kogi ya bayyana Yahaya Bello a matsayin dan takarar da ya fi cancanta ya gaji.
Buhari Ya bayyana cewa, ta fuskar ilimi da gogewa da aiki, to lallai Yahaya Bello ne zai iya zama magajin Buhari mai nagarta.
Sanatan ya dage kan cewa, gwamna Yahaya zai inganta abubuwa da dama suka tabarbare a Najeriya.
Sanata Smart Adeyemi (APC – Kogi ta yamma) ya bayyana Yahaya Bello a matsayin dan takarar shugaban kasar Najeriya da ya fi cancanta da gadon shugaba Buhari a zaben 2023, kuma ya daga Najeriya ta fuskar karfin tattalin arzikin duniya.
Read Also:
Sanatan na Kogi ya bayyana gwamnan na Kogi a matsayin gwamna matashi mai dimbin kuzari, da basirar ilimi da sanin makamar aiki tare da tarihi mai kima, ya kara da cewa yana da abin da zai kai kasar nan zuwa tudun na tsira, Daily Sun ta ruwaito.
Da yake rokon ‘yan Najeriya da su yi la’akari da burin zama shugaban kasa na Gwamna Bello, Sanata Adeyemi ya ce idan aka ba shi dama gwamnan zai hada da nasarorin gwamnatin Buhari.
Sanatan yayin da yake amsa tambayoyi jiya daga manema labarai bayan wani shirin karfafawa da ya samar wa mata masu juna biyu 1,000 a mazabarsa, ya bayyana Gwamna Bello a matsayin shugaba mai adalci wanda ke tsoron Allah ya wajen jagoranci.
A cewar sanatan, jahar kafin gwamnatin Bello ta kasance a gurbace da nuna son kai, kabilanci da nadin mukamai; kuma tun lokacin da ya hau karagar mulki ya mayar da adalci da daidaito ya zama abin kallo.