Ya Zama Wajibi mu Magance Matsalolin Matasa – Gwamnonin Arewa

Gwamnonin jihohin arewa sun ce a shirye suke da su saurari matasan arewa.

Shugaban gwamnonin, Simon Lalong ne ya fadi hakan a wani taro da suka yi a Kaduna.

Gwamnan jihar Filaton ya ce wajibi ne sauraron matasa don neman cigaba Gwamnonin jihohin arewa sun ce a shirye suke da su saurari matasan yankin a kan matsalolin da suke fuskanta.

Shugaban kungiyar gwamnonin arewa, Simon Lalong, ya fadi hakan a ranar Laraba a Kaduna yayin taron rantsarwar kwamitin matasa, wacce aka kirkira musamman don samar da mafita ga yankin.

A wata takarda da jami’in hulda da jama’ar gwamnan, Macham Makut ya saki, ya ce wajibi ne samar da ayyukan yi, kawar da jahilci, ta’addanci da talauci ga matasa ta hanyar kirkirar kwamiti.

A cewarsa, an kirkiri kwamitin, wacce Sarkin Zazzau, Alhaji Ahmed Bamalli yake jagoranta, sakamakon taron da masu ruwa da tsakin arewa suka yi, The Punch ta wallafa.

A cewar Lalong, “Matasa sun fi kowa yawa a kasar nan, don haka su ne masu ruwa da tsaki a kasar nan.

“Wajibi ne a sauraresu, kuma a yi amfani da shawarwarinsu don tafiyar da mulki yadda ya kamata.

“Wajibi ne a matsayinmu na shugabanni mu janyo matasa a jikinmu, don sanin matsalolinsu.”

Sarkin Zazzau ya tabbatar da cewa kwamitin za ta tabbatar da cewa ta dage wurin tallafawa da taimaka wa matasa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here