Magance Talaci: Ya Kamata Matasa su Tashi su Nemi Ilimin Fasaha da Sana’o’in Zamani – Pantami

 

Katsina – Tsohon ministan sadarwa da tattalin arzikin zaman, Farfesa Isa Pantami ya bayyana wasu alkaluma masu ban tsoro game da talauci a Najeriya.

Pantami, wanda yana ɗaya daga cikin manyan malumman Musulunci a Najeriya ya ce mutum miliyan 88.4, kimanin kaso 45% na al’ummar ƙasar nan na rayuwa cikin matsanancin talauci.

Kalaman Sheikh Isa Pantami na zuwa ne a daidai lokacin da Najeriya ke fama da tsadar rayuwa da taɓarɓarewar tsaro, kamar yadda Leadership ta ruwaito.

Tsohon ministan ya jaddada bukatar ƴan Najeriya musamman matasa su tashi tsaye, su nemi gogewa a fannoni daban-daban na ilimin zamani da fasaha.

Pantami ya bayyana haka ne yayin a yake gabatar da wata lakca da aka shirya a bikin cikar jihar Katsina shekara 37 da kafuwa.

“Talauci ya fi yawa a Arewa” – Farfesa Pantami

Ya ce akasarin wadanda ke fama da matsanancin talauci ƴan Arewa ne, wanda hakan ya nuna buƙatar matasa su tashi su nemi ilimin fasaha da sana’o’in zamani.

Fitaccen malamin ya ƙara da cewa a zamanin yanzu, samun takardar karatu ba za ta wadatar da mutum ba, inda ya roƙi matasan da suka gama karatu su duba wasu damarmakin.

A cewarsa, aikin gwamnati da matasa ke nema ido rufe bai wuce kaso 5% na damarmarkin ayyukan da ke akwai ba.

Pantami ya jero hanyoyin samun nasara

Pantami ya ce bincike ya nuna fasahar AI za ta samar da ayyuka miliyan 95 daga nan zuwa 2025, wanda zai maye gurbin ayyuka miliyan 83.

Domin samun nasara, Pantami ya lissafa wasu manyan fannoni da ake so mutum ya samu kwarewa a kansu da suka hada da; zamantakewa, sarrafa tunani da kuma warware matsaloli.

Gwamna Umaru Radda na Katsina ya godewa Pantami bisa amsa gayyata, inda ya ce gwamnatinsa ta riga ta bullo da wasu tsare-tsare da za su inganta goben jihar.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here