Kano: Wani Magidanci ya yi Garkuwa da Diyarsa

Hausawa kan ce ‘in da ranka ka sha kallo’ na abubuwa iri daban-daban.

A yayin da ake korafi da cece-kuce a kan yadda masu garkuwa da mutane suka addabi arewa, wani mahaifi a Kano ya ce diyarsa ta cikinsa.

Bayan ya yi garkuwa da ita, ya kira matarsa tare da neman ta gaggauta biyan kudin fansa N2m ko kuma a kashe diyarta Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta kama tare da gurfanar da wani magidanci, Fahad Ali, bisa zarginsa da yin garkuwa da diyarsa, mai shekaru hudu, tare da neman N2m a matsayin kudin fansarta daga wurin matarsa, mahaifiyar yarinyar.

Dan sanda mai gabatar da kara ya sanar da kotun majistare da ke sansanin alhazai cewa mahaifiyar yarinyar ce ta fara sanar da rundunar ‘yan sanda cewa an sace diyarta tare da yin garkuwa da ita.

A cewar dan sandan, mahaifiyar yarinyar mai suna Shamsiyya Mohammed ta shaidawa rundunar ‘yan sanda cewa wanda ya sace diyarta ya kirata a waya tare da neman miliyan biyu a matsayin kudin fansar diyarta.

Shamsiyya ta ce babu dadewa da sace yarinyar, a ranar 29 ga watan Satumba, ta samu kiran waya tare da sanar da ita cewa ko ta biya kudin fansa miliyan biyu ko kuma a kashe yarinyar.

Sai dai, bayan rundunar ‘yan sanda ta shafe sati biyu ta na gudanar da bincike, ta gano cewa mijin Shamsiyya, Fahad Ali, shine ya yi garkuwa da yarinyar, wacce aka samu tare da shi.

Bayan an gama karanta tuhumar da ake yi masa a gaban kotu, Fahad ya ce shi sam bai aikata wani laifi ba. Alkaliyar da ta saurari shari’ar, Sakina Aminu, ta bayar da umarnin a tsare Fahad a gidan gyaran hali har zuwa ranar, 24 ga watan Nuwamba, da za’a cigaba da sauraron karar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here