Yadda Mahaifi ya yi Sanadiyyar Kashe ɗansa a Jahar Kano

 

Yan sanda a Kano sun tabbatar da kama uban da ya kashe ɗansa ta hanyar lakada masa duka saboda zarginsa da sata.

Yan sandan sun ce an tsare mahaifin an tura shi sashin binciken manyan laifuka bangaren kisan kai ana bincike.

Mahaifiyar yaron, wadda ta dade da rabuwa da mahaifin ta bayyana yadda yaron ya zo mata cikin mawuyacin hali.

Wasu da abin ya faru a kan idonsu sun bayyana yadda wani ya yi yunkurin hana mahaifin dukan yaron amma bai yi nasara ba Rundunar yan sanda a jahar Kano ta ce tabbatar da kama wani magidanci da ake zargi da halaka dansa mai suna Auwalu Awaisu mai shekaru 19 sakamakon lakada masa duka a ranar Juma’a na makon da ta gabata.

Yan sandan sun ce Auwalu ya riga mu gidan gaskiya a ranar Litinin a Asibitin Murtala da ke Kano sakamakon dukan da mahaifinsa ya yi masa a ka da cikinsa, kamar yadda BBC ta ruwaito.

Mahaifin ya yi wa dansa duka ne kan zarginsa da sace masa kaya a shago.

Acewar wani da al’amarin ya faru a kan idonsa, usman kabiru yace suna zaune suka ga mahaifin yana dukan yaronsa amma basu san dalili ba kuma basu tafi sun taimaka masa ba ganin abu ne tsakanin da da mahaifinsa.

“Muna zaune a cikin shago a nan wurin sai muka ji yana dukan yaronsa a cikin shago, sunan shi Auwalu amma an fi saninsa da Abba, mun tsaya a waje a nan wurin yana ta dukan yaron badai wanda ya je wurin sai makwabcinsa mai wankin hula, ya zo ya same shi, ya ce mishi … ya dai masa magana, ni banji abinda ya fada masa ba, amma na ji lokacin da shi mahaifin ya ke masa tsawa ya ke ce masa ya fita masa a shago, ganin haka yasa muma ba mu tafi wurin ba,” a cewar Kabiru.

Hajiya Goshi Muhammad, mahaifiyar yaron wadda ta dade da rabuwa da mahaifin tsawon lokaci ta ce yaron ya zo mata cikin mawuyacin hali ta tambaye shi abinda yafaru, sai ya fada cewa mahaifinsa ne ya doke shi saboda wai bai ga ‘mansa ba guda biyu’.

Yaron ya shaidawa mahaifiyarsa cewa mahaifinsa ya yi ta dukansa a kai da ciki duk da cewa ya fada masa ba shine ya sace kaya a shagon ba.

Rundunar yan sandan Kano ta bakin kakakinta ya ce mahaifin yaron yana hannunsu,an mika shi sashin binciken manyan laifuka, bangaren kisar kai ana cigaba da bincike a kansa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here