ALLAH ya yi wa Mahaifin Albani Zariya Rasuwa

Inna lil Laahi wa inna ilaiHi Raaji’un! Allah ya yiwa mahaifin marigayi Sheikh Auwal Albany Zariya rasuwa, Sheik Dr Isa Ali Ibrahim, ya bayyana.

Dr Isa, wanda shine ministan sadarwa, ya bayyana hakan ne a shafinsa na Facebook da safiyar Laraba, 18 ga watan Nuwamba, 2020.

Ya bayyana cewa marigayin ya rasu ne yau Laraba.

Ya yi addu’an Allah ya jikansa da rahama da kuma dukkan iyayenmu da malamanmu.

A cewarsa: “Allah Ya jikan mahaifin marigayi Shaykh Muhammad Auwal Adam Albani Zaria, Wato Malam Adamu. Yau Allah Ya dauki rayuwarsa.”

“Allah Ya jikan dukkan iyayenmu da malamanmu, sannan Ya kyautata namu bayan na su.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here