Allah ya Yiwa Mahaifiyar Sheikh Kabiru Gombe, Rasuwa

Inna lillahi wa inna ilaihi raji’un – Shahrarren Malamin addini kuma sakataren kungiyar Jama’atul Izalatul Bid’a WaIqamatus Sunnah, JIBWIS, Sheikh Kabir Haruna Gombe, ya yi rashin mahaifiyarsa, Fatima Abdullahi-Haruna.

Hajiya Fatima ta rasu ne bayan shekaru 75 a duniya. Diraktan dandalin sada zumuntan JIbwis,
Ibrahim Baba-Suleiman, ya sanar da hakan a shafin Facebook da yammacin Alhamis, Daily Nigerian ta gano.

A cewarsa, Hajiya ta rasu ne da yammacin Alhamis a wani asibiti dake jihar Gombe bayan dogon rashin lafiya. Ya kara da cewa za’ayi jana’izarta bayan Sallar Juma’a ranar 30 ga wata a Masallacin JIBWIS dake Bolari, jihar Gombe.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here