Muhammadu Sanusi II: An yi Garkuwa  da Dan Uwan Tsohon Sarkin Kano

Masu garkuwa da mutane suna cigaba da cin karensu babu babbaka a titin Abuja zuwa Kaduna duk da yakarsu da ake yi.

A makon da ya gabata, sun sace yaron ‘yar uwar tsohon sarkin Kano, Sunusi Lamido Sunusi, mai suna Abdullahi, a hanyarsa ta komawa Kano kan titin Abuja zuwa Kaduna.

Wata majiya mai karfi ta ce sun gama tattara kudaden da masu garkuwa da mutanen suka bukata amma sun rasa lambar da za su kira su Masu garkuwa da mutane sun sace ‘dan ‘Yar’uwan tsohon sarkin Kano, Muhammadu Sunusi II, Daily Trust ta wallafa.

Kamar yadda bayanai suka kammala, masu garkuwa da mutane sun sace Abdullahi, wanda aka fi sani da Yaya Baba, a hanyarsa ta zuwa Kano a titin Abuja zuwa Kaduna a makon da ya gabata.

Duk da dai ba a samu wani bayani daga ‘yan sandan ba, wata majiya mai karfi ta ce basu so maganar ta fito waje ba.

Majiyar wacce take da kusanci da iyalin tsohon sarkin, ta ce masu garkuwa da mutanen sun tattauna da iyalin, inda suka nemi kudin fansa.

Amma bai sanar da nawa suka bukata ba.

Yace iyalin sun tattaro kudaden amma sun rasa lambar da za su sanar da masu garkuwar, kuma har yanzu basu sake tattaunawa da su ba.

Direbobin motocin haya masu bin hanyar Abuja zuwa Kaduna suna yawan korafi a kan yadda masu garkuwa da mutane suke tare mutane a hanyar.

A cewar direbobin, masu garkuwa da mutane sun fi tare mutane tsakanin 5 zuwa 7 na safe, da kuma 7 zuwa 9 na dare.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here