Jawabin Mata Mai Ciki da ta Haihu a Gurin ‘Yan Bindiga

 

Washegarin ranar bikin Kirsimeti, an yi garkuwa da wata yar shekara 22 mai tsohon ciki daga kauyenta a Katsina.

Da take bayyana halin da ta shiga, Suwaiba Naziru ta ce sun yi tattaki na tsawon kilomita sannan suka tsere kan babura zuwa mafakarsu.

Suwaiba ta haifi diya mace yayinda take a hannun wadanda suka sace ta wadanda suka sama mata dukkan abunda take bukata na haihuwa.

Yan bindiga a ranar Asabar, 26 ga watan Disamba, 2020, da misalin karfe 8:00pm sun kai hari Biya Ki Kwana da ke karamar hukumar Batsari, jihar Kaduna.

Yan bindiga sun yi garkuwa da Suwaiba Naziru, wacce ke da haihuwa daya da kuma tsohon ciki tare yar tata mai shekaru biyu.

Har ila yau an sace mata 10 da yara biyu yayinda aka harbi wasu matasa biyu.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here