Matsalolin kasar Nan : Dole ne Majalisar Kasa Tayi Wani Abu Game da Lamarin ko Kuma su Rufe Majalisar – Sanata Smart Adeyemi

 

Halin da Najeriya ke ciki ya batawa Sanata Smart Adeyemi rai har ya kusan yin kuka yayin da yake magana da abokan aikin sa.

A cewar dan majalisar daga jahar Kogi, dole ne majalisar kasa tayi wani abu game da lamarin ko kuma su rufe majalisar.

Da yake ci gaba, ya ce babu bukatar ‘yan majalisar su yi kamar basu san halin da ake ciki ba, inda ya dage cewa kasar na zubar jini Sanatan da ke wakiltar Kogi ta Yamma a Majalisar Tarayya, Sanata Smart Adeyemi ya yi kira ga takwarorinsa da su rufe majalisar idan ba za su iya magance matsalolin kasar ba.

Sanatan ya bayyana haka ne yayin da yake jawabi a zauren majalisa a cikin wani bidiyo da jaridar Legit.ng ta gani kuma jaridar Punch ta buga.

Ya ce:

“Kawai mu rufe majalisar kasa idan har ba za mu iya samar da tsaro ga kasar nan ba. Kasar mu tana zubda jini. Mutane suna cikin talauci. Mutane suna jin yunwa. Ba za mu iya yi kamar bamu san halin da ake ciki ba, kowace rana, mutane suna mutuwa. Dole ne mu tashi tsaye.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here