Abia: Mambobin Majalisar Wakilai Daga PDP Zasu Koma APC

 

Ficewar wasu mambobin majalisar wakilai daga Jam’iyyar PDP zuwa APC ta haddasa cece-kuce a zauren majalisa.

Wani rahoto ya gano cewa akwai yiwuwar samun karin wasu mambobin majalisar da zasu koma APC a cikin satin nan.

Sauyin shekar mambobin ba zai rasa nasaba da shirye-shiryen zaben shekarar 2023 ba.

Idan za’a iya tunawa, a cikin shekarar da ta gabata, 2020, an samu ‘yan siyasa, musamman a cikin zauren majalisar wakilai ta tarayya, da suka canja sheka daga PDP zuwa jam’iyyar APC ko kuma daga APC zuwa PDP.

Ko a ranar 15 ga watan Disamba, 2020, ‘yan majalisar wakilai biyu, Hon. Ali Datti Yako, daga Kano, da kuma Danjuma Shittu daga Taraba, sun fice daga asalin jam’iyyarsu, PDP, zuwa jam’iyya mai mulki ta APC.

Shugaban majalisar, Femi Gbajabiamila, ne ya karanta wasikar ficewar tasu lamarin da ya janyo hayaniya a majalisar daga ya’yan jam’iyyar PDP wadanda suka nemi a bayyana kujerun mambobin a matsayin wacce bata da wakili a zauren majalisar.

Sai dai shugaban majalisar, Femi Gbajabiamila, ya ce kotu ce kaɗai ke da hurumin yin hakan.

Ya kuma tuna musu a baya cewa tsohon shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki, da na wakilai, Yakubu Dogara, sun fice daga APC, sun koma PDP.

“Kun nemi da a ayyana kujerar shugaban majalisar dattijai da kakakin majalisar wakilai kujerun da ba su da wakilci lokacin da suka fice daga APC?

“Shin ni ko kotu ne ke da damar fassara kundin tsarin mulki? Ni ba kotu ba ne” in ji kakakin majalisar wakilai, Femi Gbajabiamila.

Jaridar Vanguard ta gano cewa akwai alamun samun ƙaruwar waɗanda za su sauya sheka zuwa jam’iyyar APC a cikin zauren Majalisar daga jihar Abia a wannan satin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here