Gwamna Makinde ya Naɗa Sabon Mataimakin da Zai Nemi Tazarce da Shi a 2023
Saɓanin da ya shiga tsakanin gwamnan Oyo, Seyi Makinde, da mataimakinsa ya jawo gwamnan ya fasa neman tazarce tare da shi a 2023.
Gwamnan ya bayyana ɗaukar sabon wanda zai zama mataimakinsa, Bayo Lawal, yayin da zai nemi tazarce a zaben 2023.
Mataimakin gwamna na yanzun, Injiniya Olaniyan, ya yi zargin cewa Uban Gidansa ba ya tafiya da shi a harkokin gwamnati.
Oyo – Yayin da ake ta shirye-shiryen tunkarar 2023, gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya aje mataimakinsa na yanzu, injiniya Rauf Olaniyan, a matsayin wanda zai nemi tazarce tare da shi.
Maimakon haka, gwamnan ya zaɓi shugaban hukumar gidaje ta jihar Oyo, Bayo Lawal, a matsayin sabon wanda zai taimaka masa a zaɓen gwamnoni na 2023.
Leadership ta rawaito cewa Makinde ya zaɓi Lawal ya zama mataimakinsa ne a gaban wasu mutum biyu, waɗan da aka yada jita-jitar mai yuwuwa ɗayan su ya maye gurbin Olaniyan.
Read Also:
Lawal, wanda ya fito daga yankin ƙaramar hukumar Irepo na jihar Oyo, ya rike kujerar Antoni Janar na jihar kuma an naɗa shi a shekarar 1999 karkashin mulkin tsohon gwamna Lam Adesina.
Haka nan kuma, Gwamna Seyi Makinde a zangon mulkinsa na yanzu, ya sake naɗa shi shugaban hukumar gidaje ta jihar Oyo.
Meyasa gwamnan ya ɗauki wannan matakin?
Gwamna Makinde da mataimakinsa Injiniya Olaniyan ba su ɗasa wa a yan kwanakin nan da suka gabata.
Injiniya Olaniyan, wanda ya yi zargin gwamna ya maida shi saniyar ware, ya ce bai tsoma kansa cikin zaɓukan fitar da yan takara a kujeru ɗaban-daban da ya gudana jihar ba
. Mataimakin gwamnan ya ƙara da cewa raɗe-raɗin zai sauya sheka zuwa wata jam’iyya ya yaɗu kamar wutar daji saboda ya yi gum da bakinsa bai tanka ba.
Da yake tsokaci kan zaɓukan fidda gwani da suka zakulo yan takarar da jam’iyyar PDP ta tsayar a babban zaɓen 2023 da ke tafe, Olaniyan ya ce:
“Bai kamata ku tsaya kuna hasashe ba saboda a ranar Sallah na faɗa wa mutane gaskiyar abin da ke cikin zuciyata.”