Batun Albashi: Majalisar Dokoki ta Saka Matakan Tsaro Kan Zanga-Zangar Ma’aikatan Majalissar

 

Ma’aikata a majalisar dokoki sun fusata, sun shirya zanga-zanga don neman hakkinsu na albashi.

Majalisar dokoki ta tsaurara tsaro a harabar majalisa bisa tsoron abin da ka iya biyo bayan zanga-zanga.

Ma’aikatan sun koka kan yadda suke bin bashi mai yawa daga gwamnati, wannan ya dauki tsawon shekaru.

Wani rahoto da jaridar The Nation ta fitar na nuni da cewa an tsaurara matakan tsaro a ciki da wajen Majalisar Dokoki ta kasa domin dakile wata zanga-zangar da wasu masu taimaka wa majalisar suka shirya.

Majalisar a safiyar ranar Litinin, Litinin, 27 ga watan Satumba, ta tsaurara matakan tsaro bayan ma’aikata karkashin kulawar ma’aikatan majalissar suka tunzura don gudanar da zanga-zanga kan batun albashinsu.

Jami’an tsaro da suka hada da masu kwantar da tarzoma da ‘yan sanda na yau da kullum, ma’aikatan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS) da sauran jami’an tsaron majalisa duk hallara don kula da hanyoyin shiga da fita daban-daban a harabar majalisar.

An kuma lura cewa ba a rufe kofofin da ke kaiwa dakin shiga fadar White House daga dakunan majalisar dattawa da na wakilai ba amma jami’an tsaro na gadinsu.

Musabbabin wannan zanga-zangar

Ku tuna cewa mataimakan ‘yan majalisun dokokin Najeriya sun kudurta dakatar da ayyukan majalisar daga ranar Litinin, 27 ga watan Satumba, sakamakon rashin biyansu albashi da alawus-alawus na naira biliyan 3.1, inji rahoton PM News.

Ma’aikatan majalisar suna ikirarin cewa babban bashin ya samo asali ne daga bashin albashi na naira biliyan 1.35 da kuma biliyan N1.75 na kari da aka yi na mafi karancin albashi.

Mataimakan sun kara da cewa yayin da har yanzu mataimaka 1,300 ke bin bashin albashi, ko da daya daga cikin ma’aikatan 2, 345 a NASS bai sami karin da aka yi na mafi karancin albashi ba tun watan Yunin 2019.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here