Hukuncin da aka Yanke wa Malamar Jinya da Take wa ƙananan Yara Kisan ɗauki ɗai-ɗai
An yanke hukuncin ɗaurin rai-da-rai ga wata ma’aikaciyar jinyar jarirai, Lucy Letby, wadda ita ce ta fi yi wa ƙananan yara kisan ɗauki ɗai-ɗai a tarihin baya-bayan nan na Birtaniya.
An yanke mata hukunci ne bayan samun ta da laifin kashe jariri bakwai, da kuma yunƙurin kashe ƙarin shida a wani asibitin yara da ke Countess of Chester.
Da gangan, Lucy Letby ta riƙa yi wa jarirai allura da sauran iska a cikin sirinji, kuma ta riƙa yi wa wasu ɗura da ƙarfi, sannan ta bai wa jariri biyu guba da sinadarin insulin.
Bayan yanke mata wannan hukunci, Lucy Letby ba ta nuna wata alamar nadama ba.
A yazu dai Letby za ta shafe tsawon gaba ɗayan rayuwarta a tsare, inda ta zama mace ta huɗu a Birtaniya da aka taɓa yankewa irin wannan hukunci, wanda shi ne mafi tsanani da ake yankewa mai laifi.
Alƙalin kotun Mai shari’a Goss, ya bayyana laifin da Lucy ta aikata a matsayin “babban abin ƙyama”.
Ya ce “ta aikata abin da ya saɓa da tunanin ɗan’adam mai cikakken hankali, da ya san kimar lura da jarirai, kuma babbar cin amanar waɗanda suka yarda da aikin ma’aikatan lafiya ne”.
Alƙalin ya bayyana ta a matsayin maras tausayi, wadda ke sanya damuwarta cikin aikinta.
Lauyan da ke kare ta, Ben Myers KC, ya ce “tun bayan fara shari’ar Lucy ta ƙi musanta aikata laifin da ake zargin ta da aikatawa, dangane haka ba shi da wani mataki da zai ɗauka da zai iya kai wa ga rage tsawon hukuncin da aka yanke mata”.
Harabar kotun ta cika maƙil da iyayen da ma’aikaciyar jinyar ta halaka wa jarirai, har ma wasu sun yi sharɓar hawaye a lokacin da alƙalin yake karanta hukuncin da ya yanke wa mai laifin.
An ga wasu daga cikin masu sauraren ƙara rai a ɓace lokacin da suka saurari bayanan alƙalin.
Read Also:
Wata uwa da ita ma, ta rasa ɗanta ta ce “akwai takaici a ce akwai mutumin da zai iya aikata irin wannan mummunar aika-aika”.
Ita ma wata mahaifiya da aka kashe jaririnta cike da baƙin ciki, ta sanar da kotun cewa, “game da mutuwar yaronta, tana ganin lamarin kamar a cikin wani fim ɗin ban tsoro”.
Haka zalika, wata uwa da ke rungume da zomon wasa na yara, ta sanar da kotun cewa “abin da Lucy Letby ta aikata, mugunta ce da kuma babban abin kunya ne sakaci a matsayinta na malamar jinya da aka bai wa amana”.
Su ma iyayen wata jaririya da aka bayyana sunanta da Baby G, wadda ita ce bakwaini mafi ƙanƙanta a cikin dukkan jariran, wadda nauyinta bai fi giram 535, sun faɗa wa kotun cewa: “Allah ya raya ta” amma sai “ta faɗa hannun shaiɗanu”.
Kimanin mutum 70 ne aka taɓ yankewa irin wannan hukunci na ɗaurin rai-da-rai, inda ake ci gaba da duba lafiyar ƙwaƙwalwar huɗu a asibiti. Idan aka yanke irin wannan hulunci, ba a taɓa sauya shi ba, sai dai bisa wasu dalilai na ba sabon ba.
Sauran matan da aka taɓa yankewa irin wannan hukunci sakamakon yi wa mutane kisan ɗauki ɗai-ɗai, akwai Rose West da Joanna Dennehy, sai kuma Myra Hindley, wadda tun a wancan lokacin ta riga mu gidan gaskiya.
Jagoran jam’iyyar adawa ta Labour, Keir Starmer, ya yi kira ga gwamnati ta tilasta wa masu laifin da ake yanke wa hukunci su riƙa fuskantar waɗanda aka aikata wa laifi, ganin Letby ta ƙi bayyana a gaban kotu lokacin da aka yanke mata hukunci.
Ya ce “Ina son ganin an ɗauki mataki cikin gaggawa a wannan shari’a, saboda iyayen waɗanda lamarin ya shafa sun shiga mummunar damuwa.
“Muna neman a samar da sauyi a doka wanda zai tilasta wa masu laifi, su saurari hukuncin da ake yanke musu”, in ji shi.
Shi ma Firaministan Birtaniya, Rishi Sunak, ya ce gazawa ce da kuma tsoro a ce waɗanda aka yanke wa hukunci a cikin kotu, su ƙi fuskantar iyalan da suka aikata wa laifi.