Mamman Daura Na Daga Cikin Mutanen Kirki – Buhari

Mamman Daura na daya daga cikin mutanen kirkin da mutane ke yi wa mummunar fassara, cewar shugaba Buhari.

Ya ce Mamman yana da halaye nagartattu, kamar hakuri, juriya, fasaha, taimako, jajircewa da kuma dumbin ilimi.

Shugaban kasar ya fadi hakan ne a ranar da Mamman ya cika shekaru 81 a duniya, inda yayi masa fatan alkhairi Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya taya Malam Mamman Daura murna a ranar da ya cika shekaru 81 da haihuwa, har yake cewa “Mutane da dama suna yi wa babban dan jaridar mummunar fassara.”

Malam Daura dan ‘yar uwar Buhari ne kuma babban dan kungiyar Kaduna Mafia ne, taron manyan ‘yan kasuwa, ma’aikatan gwamnati, masu fasaha da kuma manyan sojojin arewacin Najeriya.

Shugaba Buhari, ya saki wata takarda ranar Talata ta hannun kakakinsa, Garba Shehu, inda yace “Mutanen Daura yana fuskantar kalubale, saboda duk wani babban mutum ba a yaba wa kokarinsa, hasali ma caccakar jama’a tana bin jijiyoyinsa.”

Kamar yadda Daily Trust ta wallafa, shugaban kasar ya ce, “Ba zai yiwu mutum ya zauna tare da Mamman ba, bai karu da ilimi, fasaha da gogewarsa ba.”

Shugaban kasar ya ce “cikin halayen Mamman da mutane ba su yaba wa sune saukin kansa, hakuri da jajircewarsa wurin taimakon na kusa da na nesa da shi.

“A yau da kake cika shekaru 81 a duniya, ina fatan Allah ya azurta ka da lafiya da tsawon kwana yayin taimakon Najeriya da al’umma.Kai ne tushen ilimi da fatan al’umma. Muna matukar alfahari da kai.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here