Tukur Mamu ya Magantu Bayan an Kama Shi a Masar
Matawallafin jarida, Tukur Mamu ya magantu da jaridar Najeriya bayan da aka kama shi a kasar Masar.
Ya ce ba a kama shi da kayan aikata laifi ba, don haka bai jin tsoron komai da zai iya faruwa dashi.
Hukumomin kasar Masar sun shirya dawo da Mamu Najeriya bisa umarnin gwamnatin Najeriya.
Alkahira, Masar – Fitaccen dan jarida kuma wallafin kafar labarai a Arewacin Najeriya, Alhaji Tukur Mamu dake zaune a Kaduna ya magantu bayan da jami’an tsaro suka kwamushe shi a kasar Masar.
A yau Laraba 7 ga watan Satumba ne aka tashi da labarin kame Mamu a birnin Alkahira na kasar Masar bisa umarin gwamnatin Najeriya.
Mamu dai na daya daga cikin mutanen dake tattaunawa da ‘yan bindigan da suka sace mutane da yawa a jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna.
A bayanan da ya bayar, Mamu ya ce yana kan hanyarsa ta zuwa Umrah ne kasa mai tsarki, inda aka kama shi a filin jirgin Alkahira, kuma za a dawo dashi Najeriya cikin sa’o’i 24.
Read Also:
Babu wani abu da aka kama ni dashi, inji Mamu Da yake zantawa da jaridar Daily Trust a lokacin da yake cikin jirgin da za a dawo dashi Najeriya, Mamu ya ce ba a same shi da wani abu na aikata laifi tare dashi ba.
Ya kara da cewa hukumomin kasar Masar sun bayyana masa cewa ba su da wata hujjar ci gaba da tsare shi.
Ya shaidawa Daily Trust cewa:
“Akan hanyata ta zuwa Alkahira – Masar nake amma inda na nufa Saudiyya ne domin na yi Umrah tare da wasu ‘yan uwana.
“An ajiye ni tsawon sa’o’i 24 a filin jirgin saman Alkahira bisa umarnin gwamnatin Najeriya.
“Ba a ci zarafi na a filin jirgin saman Najeriya ba har sai da na isa birnin Alkahira inda jami’an tsaro dake wurin suka ce min hukumar tsaro ta farin kaya ta Najeriya (DSS) ta ba da umarnin a kama ni.
“An tsare ni ne tare da ahali na tsawon yini guda a filin jirgin saman Alkahira.”
“Yanzu haka sun kama jirgi na gaba domin a taho da ni da ahalina zuwa gida Kano. Na tabbata jami’an DSS za su jira saukarmu a filin jirgin saman Kano a yau (Laraba).
“Babu wani abu da nake boyewa kuma ba na jin tsoronsu (DSS) na rantse da Allah ba na tsoronsu, ina dai son duniya ta san abin da ke faruwa ne kawai.”
Gwamnatin Najeriya ta sha zargin Mamu da bin tsagin ‘yan ta’adda maimakon kare muradin gwamnati, batun da yake yawan musantawa.