Fasaha: Manoman Kano Sun Yabawa Tsarin Noman Zamani na KSADP

Shirin bunkasa noma da kiwo na jahar Kano (KSADP) nakara bunkasa musamman ta fannin bunkasa abinci da tattalin arzikin manoma. daya cikin manoman ne ya bayyana haka a garin Laraban Gadon Sarki dake karamar hukumar Warawa a nan jahar Kano.

A lokacin da cibiyar Sasakawa Africa Association guda daga cikin wadanda suke gabatar da shirin na KSADP, a lokacin ta shirya wani gagarumin taron nuna amfanin gona a garin Tofai dake karamar hukumar Gabasawa da kuma garin Larabar Gadon Sarki dake karamar hukumar Warawa.

Manomin ya tabbatar da cewar sun samu gagarumin cigaba ta fanni amfanin gona da sabbin dabarun zamani da shirin ya zo musu da shi, inda ya Kara da cewar babu shakka za su cigaba da amfani da wa dannan dabaru da kuma sababbin irirrikan da ake zuwar musu da shi.

Taron ya samu halarta mataimakin shugaban cibiyar Sasakawa na kasa Dr. Abdulhamid Gambo da shugaban shirin KSADP a Sasakawa Comr. Abdurrashid Hamisu Kofar Mata, da iyayen kasa da sauran manoma.

A karshe an bukaci manoma da su cigaba da yin amfani da dabarun da suka samu a cikin shirin na KSADP.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here