Aliko Dangote ya Koma na 117 a Jerin Manyan Attajiran Duniya

 

Babban attajirin nan na Najeriya da Africa, Aliko Dangote, ya koma na 117 a jerin manyan attajiran duniya da aka fitar.

Rahoton wanda jaridar Bloomberg ta fitar ya nuna cewa Dangote ya mallaki dala biliyan $17.8bn.

Elon Musk, shine attajirin da yafi kowa kuɗi a duniya kamar yadda rahoton ya nuna da dala biliyan $194bn.

Kano – Sabon rahoton manyan attajiran duniya da jaridar Bloomberg ta fitar ya nuna cewa attajirin mai kuɗin Najeriya, Aliko Dangote ya koma na 117.

Kafin fitar da rahotonta, jaridar Bloomberg tana bincike da tattara bayani tare da lissafa dukiyar da kowane mai kuɗi ya mallaka.

BBC Hausa ta ruwaito cewa Bloomberg na yawaita fitar da rahoto game manyan mafiya arziki a duniya.

A wannan karan rahoton ya bayyana cewa Aliko Dangote, shugaban kamfanin ‘Dangote Group’ ya mallaki dukiyar da takai dalar Amurka biliyan $17.8bn.

Wanene yafi kowa arziki a duniya?

Wanda yafi kowa kuɗi a duniya a cewar rahoton shine Elon Musk, haifaffen ƙasar Africa ta kudu, wanda ya mallaki dalar Amurka biliyan $194bn.

Mutumin da yazo na biyu shine shugaban kamfanin Amazon kuma mamallakinsa, Jeff Bezoz, wanda yake da arzikin dala biliyan $194bn.

Attajiri na uku mafi kuɗi a duniya shine Bernard Arnault, ɗan kasar Faransa wanda ya mallaki dala biliyan $174bn.

A baya dai shugaban kamfanin Microsoft, Bill Gates, shike rike da matsayi na uku amma yanzun an kere shi.

Punch ta ruwaito cewa ana ganin dai kuɗin Bill Gates ya ragu ne sanadiyyar rabuwar da ya yi da matarsa Melinda Gates a yan kwanakin baya.

Mamallakin shafin sada zumunta wato Facebook, Mark Zuckerberg, shine na biyar a jerin masu kuɗin duniya inda yake da dukiyar da takai dala biliyan $135bn.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here