Masana Sun Bayyana Wanda ya Cancanci ya Gaji Shugaba Buhari a 2023

 

Hasashen masana na kara tabbatarwa cewa, Osinbajo ne ya fi cancanta da gadon kujerar Buhari.

Wannan na zuwa ne daga wata kuri’a da jaridar ThisDay ta gudanar kan shugaban da ya fi cancanta.

Masana sun bayyana nagartar Osinbajo ta fuskoki da dama wanda suke ganin shi ne mafi cancanta

Abuja – Yayin da ake tattaunawa game da wanda zai zama shugaban Najeriya na gaba a 2023, masana sun bayyana mataimakin shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo a matsayin dan takarar da yafi nagarta, kamar yadda yazo a kuri’ar da jaridar ThisDay ta yi.

Kuri’ar ya biyo bayan hirar da tsohon shugaban kasa, Janar Ibrahim Babangida yayi da gidan talabijin na Arise TV akan wanda zai zama shugaban Najeriya a 2023.

Osinbajo shi ya cancanci zama shugaban kasa

Baya ga cancantar ilimi, Babangida ya ambaci shekaru da gogewa a matsayin muhimman abubuwan da za su sa a zabi wanda zai maye gurbin Buhari a 2023, inda ya bayyana a sarari cewa ya kamata ‘yan Najeriya su zabi mutum mai kuzari wanda bai haura shekaru 60 ba.

Kuri’ar da jaridar ta wallafa a ranar Litinin ta kawo wasu fitattun ‘yan Najeriya, tare da Osinbajo cikinsu a matsayin wadanda suka cancanta su rike manyan mukamai a nan gaba.

Sauran wadanda aka kawo sun hada da Shugaban Bankin Raya Kasashen Afirka, Dakta Akinwunmi Adesina da Mataimakiyar Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Misis Amina Mohammed.

Hakazalika da tsohon mataimakin gwamnan babban bankin Najeriya, Farfesa Kingsley Moghalu, da gwamnan jahar Ekiti, Mista Kayode Fayemi, da sauransu.

Gina sharhin su kan sharuddan da tsohon shugaban na soji Babangida, su ne:

tsohon shugaban hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya, Dakta Sam Amadi, ya ce Osinbajo ya fi cancanta fiye da sauran dukkan mutane 30 da aka lissafa a cikin rahoton ThisDay.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here