Masarautar Zazzau Tayi Rashin Manya Biyu a Yau Juma’a

 

Masarautar Zazzau a ranar Juma’a ta yi rashin manya biyu kuma rana guda.

Iyan Zazzau, Bashir Aminu, da Talban Zazzau, Abdulkadir Iya-Pate, sun rasu yau Juma’a Masarautar Zazzau ta yi babban rashin da ba tayi irinta ba tun rasuwar marigayi sarkin zazzau, Alha Shehu Idris.

Manyan masu sarauta biyu suka mutu ranar juma’a.

Yayinda Iyan Zazzau, Aminu, ya rasu a wani asibitin jihar Legas kuma aka kai shi Zaria domin jana’iza, Talban Zazzau, Iya-Pate, ya rasu ne a Zariya bayan rashin lafiyan da yayi fama da shi.

Mai martaba sarkin Zazzau, Ahmed Bamalli, ya fara sanar da mutuwar Iyan Zazzau a shafin Tuwita, ranar Juma’a.

“Cikin bakin ciki da alhini muke sanar da mutuwar mai sarauta mafi karfi kuma Yarima mafi arziki a arewacin Najeriya, Alha Bashar Aminu, Iyan Zazzau,” yace.

Iyan Zazzau na daya daga cikin Yaromomin Zazzau da suka nemi kujeran Sarkin Zazzau bayan rasuwar, Alhaji Shehu Idris, amma bai samu nasara ba.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here