Rashin Sani Yafi Dare Duhu: Wasu Masoya Sun Gano Baban Su Daya

Sai da na gabatar da ita, mahaifina ya tabbatar min da cewa kanwata ce, cewar Njoroge.

Wani saurayi dan kasar Kenya yana shirin angwancewa da Wanjiku ya gano kanwarsa ce.

Mahaifinsa ya tabbatar masa da cewa Wanjiku diyar kishiyar mahaifiyarsa ce, dole aure ya fasu.

Wasu masoya 2 ‘yan kasar Kenya sun gano cewa yaya da kanwa suke, ana saura ‘yan kwanaki kadan shagalin bikin aurensu.

An umarci John Njoroge ya dakata da shirye-shiryen aurensa da Rose Wanjiku, (ba sunayensu na asali ba), bayan ya turo magabatansa, The Nation ta wallafa.

Al’amarin ya daga wa Njoroge hankali, bayan ya gano cewa ubansu daya da Wanjiku domin diya ce ita ga kishiyar mahaifiyarsa.

Kamar yadda ya bayyana wa gidan talabijin din Kameme, “Bayan da na gabatar da ita ga iyayena, mahaifina ya shaida min cewa ni yayanta ne, diya ce ita ga kishiyar mahaifiya ta.”

Njoroge ya fara soyayya da budurwar sa ne bayan ta siya takalmi a wurinsa, wanda ya kai mata har gida domin neman yada manufarsa.

Wanjiku ta bayyana tsoronta a kan fara wata soyayyar da wani. A cewarta, “Ina tsoron kara fadawa soyayya da wani, saboda kada in kara gane dan uwana ne.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here