Mata 6 da Yara 9 Sun Tsere Daga Sansanin Mayakan Boko Haram a Borno
Rahotanni daga Najeriya na cewa mata shida da yara 9 sun tsere daga sansanin mayakan Boko Haram da ke jahar Borno a arewa maso gabashin kasar.
Tashar Channels ta rawaito cewa cikin wadanda suke tsere har da mace mai cikin wata 8, da ta yi tafiya sa’a shida a cikin jejin Sambisa, kafin jami’an tsaro su ceto su.
An yi garkuwa da mutanen ne daga kauyukan Takulashi mai tarin manoma a Borno da kuma Cofure da ke Adamawa watanni da suka gabata.
Gwamnan Borno Farfesa Babagana Zulum ya shaida cewa gwamnati na yin duk mai yiwuwa domin ganin ya sada mutanen da Boko Haram suka raba da iyalansu.
 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here